1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin kasashe da dama za su hallara a taron MDD

September 19, 2025

Rikicin Isra'ila da yankin Falasdinu zai kankane taron kasashen duniya na bana da za a yi a birnin New Yorka na Amurka, inda shugabannin kasashe da dama za su halarta. Sai dai Amurka ta hana shugaban Falasdinawa dama.

Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya na birnin New York
Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya na birnin New YorkHoto: Michael M. Santiago/Getty Images

Sama da shugabannin kasashe 140 ne za su hallara a birnin New York cikin makon gobe domin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.

Matsalar jinkai da ta addabi yankin Falasdinu za ta kasance a kan gaba a tattaunawar, shekaru biyu bayan kaddamar da farmakin Isra'ila a Zirin Gaza, wanda ya samo asali daga mummunan harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Shugaba guda da ba zai halarci taron a Zahiri ba shi ne shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda Amurka ta hana biza tare da wadansu jami'ansa.

A karo na musamman, babban zauren ya kada kuri'a a ranar Juma'a domin bai wa Abbas damar yin jawabi ta hanyar bidiyo, yayin da jakadan Falasɗinu zai wakilce shi a cikin dakin taron.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW