1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugabannin nahiyar Turai za su gana a Berlin

November 17, 2025

Ganawar za ta mayar da hankali ne kan samar da cikakken iko na sadarwar zamani a Turai.

Shugabannin za su gana ne a ranar Talata a birnin Berlin na Jamus
Shugabannin za su gana ne a ranar Talata a birnin Berlin na Jamus Hoto: Leon Neal/Getty/AP/dpa/picture alliance

Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz, zai gana da takwarorinsa na Faransa da Burtaniya a birnin Berlin a daren Talata, in ji mai magana da yawun gwamnatin, ba tare da ya bayar da karin bayani ba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, zai isa Berlin tun da wuri a ranar Talata domin halartar taron koli da aka shirya kan kokarin samun cikakken iko na sadarwar zamani ta intanet a Turai.

Merz ya bukaci garanbawul ga tsarin tallafi

Bayan taron, Merz da Macron za su hadu da Firaministan Burtaniya, Keir Starmer, “a yayin liyafar cin abincin dare,” in ji mai magana da yawun gwamnatin, ba tare da bayyana abin da tattaunawar za ta mayar da hankali a kai ba.

An shirya  taron sadarwar zamani ta intanet din ne a matsayin martani ga yawan kiraye-kiryen da ake yi na bai wa Turai cikakken iko kan harkar, musamman ma yayin da fasahar AI ke taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama na duniya.

Jamus ta yi allawadai da harin Rasha kan Poland

Ganawar za ta kuma samu halartar manyan shugabannin kamfanoni ciki har da kamfanin fasahar AI na Faransa, Mistral, da babban kamfanin na'urori na Jamus SAP.