1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugabannin Sahel sun yi kira ga MDD da ta hukunta Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2024

Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakan da suka dace kan Ukraine, bisa zargin ta da goyon bayan kungiyoyin 'yan tawaye a arewacin Mali.

Shugaba Goita na Mali da Tiani na Nijar da Traore na Burkina Faso
Shugaba Goita na Mali da Tiani na Nijar da Traore na Burkina FasoHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Cikin wata budaddiyar wasika, ministocin harkokin wajen kasashen uku Mali da Nijar da Burkina Faso sun bukaci MDD da ta ladabtar da Ukraine kan ayyuka da suka danganta da zagon kasa da shisshigi da kuma karfafa kungiyoyin ta'addanci a nahiyar Afirka.  Tun a  farkon watan Agusta ne kasashen Mali da Nijar suka katse huldar diflomasiyya da kasar Ukraine, bayan da sojojin Mali da kuma kawayenta na Rasha suka kai kasa labari a yaki da 'yan aware. 

Karin bayaniMali: Ko yakin Rasha da Ukraine na fadada?

Sai dai wani jami'in leken asirin Ukraine, Andriï Yussov, ya nunar da cewa kyiv ta ba da bayanai ga 'yan tawayen domin su kai harin, amma fannin diflomasiyyar na Ukraine ta yi watsi da zargin Mali da kakkausar murya. Wata majiyar tsaron ta kasashen yammacin duniya ta tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa akwai alaka tsakanin hukumomin sojin Ukraine da 'yan awaren Mali.

Karin bayani:Tabarbarewar alakar Ukraine da Mali

Amma fannin diflomasiyyar Ukraine ya yi watsi da zargin Mali da kakkausar murya tare da tabbatar da cewa yana bin ka'idojin dokokin kasa da kasa. Sannan ta yi tir da matakin Mali da na Nijar  na yanke hulda da ita.