An kammala zaben shugaban kasar Taiwan
January 11, 2020Talla
An kammala kada kuri'un zaben shugaban kasar Tailan lami lafiya, sai dai alamu na nuna cewa Shugaba Tsai Ing-wen za ta samu damar yin mulki wa'adi na biyu saboda yi wa abokin karawarta Han Kuo-yu zarra da yawan kuri'u.
Shugaba Tsai ta jam'iyyar DPP ta dare karagar mulki a shekarar 2016, kuma ana ganin wannan zabe zai taka rawa sosai na raba gari tsakanin Taiwan da gwamnatin China mai ikirarin tsibirin na karkashin ikonta.