SiyasaAfirka
Shugabar tawagar dakarun EU ta fice daga Nijar
March 18, 2024![Sojojin EUCAP dake aikin wanzar da zaman lafiya a Sahel a wani taro a Nijar.](https://static.dw.com/image/58760298_800.webp)
Talla
Shugabar kungiyar dakarun Katja Dominik 'yar kasar Jamus da shugaban kwamitin tsare-tsaren dakarun Mads Beyer 'dan kasar Denmark sun sauka a birnin Brussels a yammacin jiya lahadi 17 ga watan Maris 2024.
Karin bayani:An bukaci wasu dakaru su fice daga Jamhuriyar Nijar
Mai magana da yawun EU ta shaidawa manema labarai cewa tuni dukkan dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Nijar suka fice daga yankin na yammacin Afrika.
Karin bayani: Sahel: Kafa rundunar sintiri ta Turai
Kimanin sojojin kawancen dakarun EU 120 ne ke aiki a Jamhuriyar Nijar wajen horas da sojojin kasar a wani yunkuri na yaki da 'yan ta'adda da 'yan bindiga harma da masu hada-hadar miyagun kwayoyi zuwa ga dakile ayyukan masu safara da mutane.