Kamaru: Mece ce makomar siyasa?
November 19, 2025
Issa Tchiroma Bakary na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga mulkin Paul Biya da kawo yanzu galibin al'ummar kasar ba su amince da nasararsa a zaben 12 ga watan Oktoba 2025 ba. Har yanzu dai wasu na ikirarin Tchiroma Bakary ne ya lashe zabe, kuma barazanar da gwamnatin Shugaba Biya ke yi musu ba za ta hana su fadin gaskiya ba.
Shugabannin kasa biyu?
Wani matashi kana mukaddashin shugaban wata karamar hukuma a Douala Serge Espoir Biyong ya nunar da cewa: "Gaskiyar ita ce, Shugaba Issa Tchiroma Bakary ya lashe zabe. Da yake yana damun wadanda ke da jami'an tsaro da sojoji da makamai, abin da yake ba su damar ci gaba da mulki da karfin tuwo ba za su taba yarda ba......"
Lauya Alice Nkom da jami'an tsaro suka yi wa gidanta kawanya jim kadan bayan nadin, ta yi kira gare shi da ya gaggauta kama aiki: "Shugaba Issa Tchiroma shi ne kadai zababben shugaban kasa a duniya da ya yi gudun hijira, inda ya kamata kuma yana kan madafun iko. Abin da suke son yi shi ne su hana shi dawowa, Tchiroma na gudun hijira a wata kasa, muna jira ya tafiyar da kasar kamar shugaban kasa daga inda yake."
Mece ce makomar 'yan adawa?
Ga manazarta kamar dan jarida Alhaji Labaran Isiyaku Bagobiri, nada fitacciyar lauya da Tchiroma Bakary ya yi babbar barazana ce ga mulkin Paul Biya. Galibin 'yan Kamaru kama daga 'yan siyasa zuwa kungiyoyin farar hula da suka goyi bayan takarar Tchiroma Bakary a wannan zabe, sun yi gudun hijira ko suna tsare kawo yanzu ba a san makomar suba.
Rahotanni na tabbatar da cewar jagoran adawa na Kamaru Issa Tchiroma Bakary na karkashin kulawar jami'an tsaron Najeriya a garin Yola na jihar Adamawa, bayan da hukumomin kasar suka ki amincewa da bukatar takwarorinsu a Kamaru na mika shi. Tun da aka rantsar da a karo na takwas Paul Biya bai nada sababbin ministoci ba, yayin da a ranar 30 ga wannan wata za a yi zaben kananan hukumomi.