Sin ta yaba da ziyarar Firamiyan Japan a kasar
October 8, 2006Talla
Shugaban kasar Sin Hu Jintao yace ziyarar da Firaministan Japan Shinzo Abe ya kai kasar Sin wani sabon shafi a dangantakar tsakanin kasashen biyu.
Shugaban na kasar Sin ya baiyana fatar cewa wannan ziyara zata inganta dukkanin huldodi tsakaninsu.
Abe a nashi bangare yace Japan da Sin sun amince cewa,ba zasu lamunta Koriya ta arewa ta gudanar da gwajin nukiliya ba haka kuma ya kamata Koriyan ta koma teburin tattaunawa na shirinta na nukiliya ba tare da wasu sharudda ba.