SIPRI: Yaduwar makamai na ta'azara rikice-rikice
December 1, 2025
Kamfanonin kera makamai, ba su taba yin ciniki irin na shekara ta 2024 ba. Wannan shi ne abin da rahoton na Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya da ke birnin Stockholm wato SIPRI ya bayyana, bayan gudanar da bincike a manyan kamfanonin kera makamai na duniya guda 100. Rahoton ya ce, kamfanonin sun samu ribar dalar Amurka biliyan 679 a bara sakamakon sayar da makamai da sauran kayayyakin aikin soja.
A cewar SIPRI hauhawar farashi ya haifar da karuwar kusan kaso shida na kudin kayayyakin yakin, idan aka kwatanta da wanda aka saya a shekara ta 2023.
Baya ga haka, a cewar rahoton yakin da ake fuskanta a sassan duniya musamman ma Ukraine, ya haifar da karuwar bukatar makamai tare da ta'azzara lamarin a shekara ta 2024 da ta gabata.
Shin Yakin Ukraine, riba ce ga masu sayar da makamai? A hirarsa da DW guda daga cikin wadanda suka fitar da rahoton Nan Tian daga cibiyar ta SIPRI ya ce: "A bangaren tsaro tabbas riba ce." Ya kara da cewa: "A shekaru biyun da suka gabata, kamfanonin kera makamai sun ci riba sosai." An samar da sababbin makamai, an kuma maye gurbin wadanda suka lalace.
Kamfanonin Jamus sun fi cin riba
Daga cikin manyan kamfanonin kera makaman 100 da aka gudanar da binciken a kansu, 39 na Amurka ne. Kamfanonin 39 sun samu kusan rabin kudin shiga na duniya daga sayar da makamai, inda suka samu karuwa ta kimanin kaso uku da digo takwas. A nasu bangaren, kamfanonin Turai 26 ban da na Rasha, sun samu kudin shiga na kaso 13.
Amma fa kamfanonin Jamus, sun yi nasarar kara kudin shigarsu da kaso 36 cikin 100. A cewar Nan Tian guda daga cikin wadanda suka gudana da binciken na SIPRI: "Kusan hakan na da alaka da matakin Rasha na mamaye Ukraine, abin da ya janyo karuwar bukatar makaman daga rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr.
Kamfanoni kamar Rheinmetall ko Diehl sun kera tankokin yaki da sauran manyan makamai, a matsayin tallafin soja ga Ukraine. Sai dai a hannu guda, suna kara bunkasa kamfanonisu ne.
Takunkumi kan yaki, bai hana kamfanonin Rasha bunkasa ba
Cikin rahoton na SIPRI, binciken da suka yi ya nunar da cewa kamfanonin kera makamai na Rasha ma sun samu ci-gaba. Ba abun mamaki ba ne, duk da cewa a bangaren fitar da makaman ta samu nakasu saboda takunkumi, amma bukatar makaman da ake da ita a cikin gida ta maye gurbi.
Sai dai akwai banbamci tsakanin yadda abun yake a Rasha da sauran kasashen, kamar yadda Nan Tian daga cibiyar SIPRI ya nunar: "Kasar na da abubuwan da ta muhimmanta na dabam, bangaren tattalin arziki ga misali da samar da kayyaki, ya koma zuwa samar da kayyakin yaki a shekaru ukun da suka gabata." Ga misali, Rasha ta kara yawan motocin atilare da kaso 420, daga shekara ta 2022 zuwa 2024. A cewar rahoton SIPRI yanzu Rasha na kera motocin atilaren miliyan daya da 300,000, maimakon 250,000 da take kerawa a baya.
Sakamakon takunkumin karya tattalin arziki na kasa da kasa da aka kakaba mata, Rasha ba ta taka rawa a bangaren sayar da makamai a ketare musamman kayan latironi na jiragen yaki.
Sai dai kuma mafarkin da aka yi na cewa hakan zai karya tattalin arzikin Moscow, bai tabbata ba a cewar Nan Tian na SIPRI: "Tabbas kasar ta samu kanta cikin halin kunci, idan aka kawatanta da kafin ta mamaye Ukraine, saboda a lokacin babu takunkumi. Sai dai kuma Rasha ta bai wa marada kunya, ta fuskar takunkumi da kuma samun masassarar tattalin arziki."
Nan Tian ya shaidawa DW cewa, ya yi amannar sauyin da aka samu ta fannin tattalin arzikin Rasha zai wahala ya sauya daga tattalin arziki a bangaren kayan yaki, koda kuwa an samu zaman lafiya na dindindin a Ukraine.