1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SIPRI: Yake-yake na kara bude kasuwar makamai

Strack Christoph | Abdourahamane Hassane SB
March 9, 2026

Tsoron da nahiyar Turai ke ji na fuskantar hare-hare daga Rasha na karuwa. Bayanan ke nan da Cibiyar Bincike Zaman Lafiya ta Duniya (SIPRI).ta bayyana cikin rahotonta na shekara game da batun cinikin makaman a duniya.

Großbritannien London 2025 | Internationale Verteidigungs- und Sicherheitsmesse DSEI
Hoto: Rasid Necati Aslim/Anadolu/picture alliance

Kasuwar makamai tana bunƙasa. Fitar da makamai a duniya ya ƙaru da kusan kashi goma cikin ɗari a cikin shekaru biyar da suka gabata idan aka kwatanta da shekaru biyar baya, a cewar wani sabon rahoto daga Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya ta Duniya da ke a  Stockholm wato (SIPRI).

Hoto: Mustafa Ciftci/AA/picture alliance

Rahoton ya nuna cewar kudaden shiga na duniya a cinikin makamai sun karu sosai a shekarar ta 2025, inda buƙatun suka samo asali  daga rikice-rikicen Ukraine da Gaza, da rikicin siyasa da na yaki. A karon farko tun daga shekarar 2018, duk manyan kamfanonin makamai guda biyar sun sami ƙaruwar kudaden shiga.

Kasuwa ta bude wa manyan kamfanonon kera makamai

Cinikin makamai na duniya yanzu ya kai kusan adadin da yake da shi kafin ƙarshen yaƙin cacar Baka a shekara ta1989. A halin yanzu, ya ragu sosai, da kusan kashi ɗaya bisa uku, har zuwa shekarun da suka biyo bayan ƙarni na 1980.

Hoto: Philipp Schulze/dpa/picture alliance

A cewar sabon rahoton na cibiyar SIPRI, Turai ita ce yankin da ya fi muhimmanci wajen shigo da makamai. Tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2020.

Turai ta kusan ninka yawan makaman da take shigowa da su sau uku, yanzu ita ce kan gaba a duniya.

Yawancin sauran ƙasashen Turai sun fara shigo da makamai masu yawa, in ji masanin SIPRI George, "don ƙarfafa ƙarfin sojojinsu a gaban barazanar da ake ganin tana ƙaruwa daga Rasha.

Tasirin yakin Rasha da Ukraine kan makamai

Hoto: Staff Sgt. N.B./dpa/picture alliance

A cewar rahoton, yawan makaman da Amurka ta kai a Ukraine a shekarar ta 2025 ya yi ƙasa sosai fiye da na shekaru biyu da suka gabata. Da  hawansa kan karagar shugabancin Amurka, Donald Trump ya rage tallafin soja da kasarsa ke bai wa Kyiv.

Ko da lokacin da kawayen Ukraine, ko kasashen Turai, Ostiraliya,da Kanada, suka haɗa kai suka sayi manyan makamai masu linzami masu kakkaɓo jiragen sama daga Amurka  don bai wa  Ukraine, SIPRI ta ɗauki waɗannan a matsayin kayan da Amurka ke fitarwa zuwa Ukraine.

Hoto: picture alliance/dpa/dpa-Zentralbild

Amurka ta ci gaba da kasancewa babbar mai samar da makamai a Ukraine, tare da Koriya ta Kudu, A duniya, ƙasashen Turai kamar Faransa, Italiya, da Jamus suma sun ƙara rawar da suke takawa a matsayin masu fitar da makamai.

Sakamakon tallafin makamai da take bai wa Ukraine,Jamus ta zarce China a cikin shekaru biyar da suka gabata, da kashi 5.7 cikin ɗari na kasuwar makamai ta duniya, ta zama ta huɗu mafi girma wajen fitar da makamai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani