Turkiyya ta zargi shugaba Emmanuel Macron na Faransa
October 10, 2019Talla
A wani cigaban kuma ministan harkokin kasashen ketare na Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya zargi shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da raba kasar Siriya, bayan Faransan ta yi Allah wadai da harin da dakarun Turkiyyan suka kai wa Kurdawan.
Kasashe da dama sun tsoratar game da yiwuwar tserewar 'yan kungiyar IS da ke tsare a gidajen yarin Siriya sakamakon wannan hari, duk kuwa da cewar shugaban kasar Bashar al-Assad ya dauki alwashin daidaita al'amura cikin kankanin lokaci.