Siriya: Birnin Raqa na shirin kubuce wa kungiyar IS
September 20, 2017
Rahotanni daga Siriya na cewa rundunar kawancen kungiyoyin tawayen kasar masu samun goyon bayan Amirka a cikin yaki da kungiyar IS ta yi nasarar karbe iko da sama da kashi 90 cikin 100 na birnin Raqa daga hannu kungiyar a wannan Laraba.
Kungiyar masu sa ido kan yakin kasar ta Siriya ta OSDH ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wasu jerin hare-hare ta sama da jiragen yakin kawancen suka zafafa a kwanaki biyu na baya-bayan nan sun tilasta wa mayakan kungiyar ta IS ficewa daga cikin akalla unguwannin birnin biyar.
Sai dai kuma ta ce mayakan na IS na ci gaba da jan daga a wasu unguwannin tsakiyar birnin, inda suke rike da wasu manya-manyan gine-ginen gwamnati da suka hada da tsohuwar hedkwatar gwamnan birnin da kuma tsohuwar cibiyar leken asirin gwamnatin kasar ta Siriya.