1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Dakarun gwamnati sun kafa tuta a Deraa

Abdourahamane Hassane
July 13, 2018

Dakarun gwamnatin Siriya sun daga tutar kasar a cikin birnin Deraa cibiyar yan tawayen da suka soma tada bali ga gwamatin Bashar al Assad tun a shekara ta 2011.

Syrien, Konflikt, Daraa
Hoto: Reuters

Masu aiko da rahotannin sun ce an ga tawagar sojoji Siriya da na Rasha da 'yan sanda tare da rakiyar 'yan jarida sun shiga birnin na Deraa bayan makwanin uku dai da dakarun gwamnatin suka kwashe suna barin wuta a yankin 'yan tawayen sun amince da wata yarjejeniyar zaman lafiya a farkon wannan wata wacce kasar Rasha ta shiga tsakani.