Siriya ta ce dakarun Iran da Hezbollah ba fita
May 23, 2018Mataimakin ministan harkokin wajen Siriya Faisal al-Meqdad ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi a wannan rana ta Laraba cewa babu batu na janyewar dakarun kasar Iran ko dakarun Hezbollah 'yan Lebanon daga kasar ta Siriya.
Dakarun sojan Iran da mayakan sakai na kungiyar Hezbollah daga Lebanon sun shiga yakin kasar ta Siriya inda suke kare bangaren gwamnati. Matakin da Isra'ila tsawon lokaci ta dade tana adawa da kasancewar dakarun na Iran manyan abokan gabatarta su kasance a kusa da kasarta. Amirka dai da ke zama babbar kawa ga Isra'ila ta yi kira na ficewar dakarun na Iran daga Siriya su kuma kawo karshe na taimakon da suke ba wa kungiyar Hezbollah.
A cewar al-Meqdad janye irin wadannan dakaru babbar matsala ce ga ci gaba da kasancewar kasar ta Siriya a matsayin kasa me 'yancin kanta. Ya kuma bayyana haka ne ga kafar yada labarai ta Sputnik ta kasar Rasha.