1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Hari kan sojojin gwamnati a Homs

Ramatu Garba Baba SB
April 9, 2018

An zargi Gwamnatin Siriya da laifin amfani da makami mai guba bayan da ta kaddamar da hari a yankin Gabashin Ghouta a sanadiyar wargajewar yarjejeniya da bangarorin masu rikici da juna suka kulla.

Syrien Raketenangriff
Hari kan wani sansanin sojan saman Siriya a HomsHoto: picture-alliance/Photoshot

A  wata sanarwar da kungiyar likitoci a kasar ta fitar ta ce mutane fiye da dari biyar da aka kai asibiti a sanadiyar matsalar numfashi duk sun shaki sinadarin gas a wannan yankin Ggwamnati ta Siriya dai ta nesantar da kanta daga wannan zargi da ake yi mata, inda ta ce ta na samun galaba kan abokan gaba saboda haka babu dalilin amfani da wani makami mai guba.

Wadanda ake zargin an saka musu bama-baman masu guba a yankin 'yan tawayeHoto: picture-alliance/AA/M. Bekkur

Batun amfani da makamai masu  gubar bayan yada hotunan harin ya matukar tayar da hankulan duniya, inda tuni ma kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya wani zama don tattauna batun a wannan Litinin. Shi kuwa Shugaba Donald Trump na Amirka gargadi ya yi na daukar tsatsaurar mataki kan gwamnatin Assad da ya zarga da hannu a harin kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter. 

Sojojin gwamnatin SiriyaHoto: Getty Images/AFP/G. Ourfalian

Rasha da ke tallafawa gwamnatin Assad don ganin ta samu nasara a rikicin kasar ta musanta zargin da ake yi wa gwamnati ta Siriya na amfani da makamai masu gubar amma ta ce abin da ya dace shi ne mayar da hanakali kan bincike a cewar ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov. Yanzu haka dai rikicin kasar na sake rincabewa bayan da kafar yada labaran kasar ta Siriya ta yada rahoton harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai da makamai masu linzami a sansanin sojin kasar da ke a garin Homs inda aka samu asarar rayukan mutane da dama.