Siriya: Majalisar Dinkin Duniya ta yi kasheidi
April 14, 2018Dangane da wannan batu ma dai Sakaraten na MDD ya dage bulaguron da ya yi niyar yi a kasar Saudiyya, domin kula da abun da zai biyo bayan hare-haren da kasashen Amirka, Faransa da Britaniya suka kai a kasar ta Siriya.
Kasar Faransa ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Jean Ives Le Drian, cewa ta yi harin da suka kai abu ne da ya dace kuma sun yi shi daidai ne laifin da Bashar Al-Assad ya aikata, domin sun kai shi ne ga muradu na gwamnatin Siriya kawai.
Tuni dai kungiyar Tsaro ta NATO cikin wata sanarwa da ta fitar da sanyin safiyar Asabar ta ce ta goyu bayan wannan hari da Amirka, Faransa da kuma Britaniya suka kai a Siriya.
A wata sanarwa da ya fitar ofishin ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya ce sun yi maraba da wannan hari da kasashen Yamma suka kai kan muradun gwamnatin Bashar Al-Assad da ake zargi da kai harin makamai masu guba a birnin Douma.