1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na ci gaba da gallazawa masu adawa da gwamnati

September 26, 2011

Tankokin yaƙin Siriya sun kai hari akan wani garin dake kusa da birnin Homs a ƙoƙarin daƙile masu boren adawa da gwamnati

Tankar yaƙin Siriya a garin Homs ranar 17.08.2011Hoto: picture alliance/dpa

Tankokin yaƙin ƙasar Siriya sun ƙaddamr da farmaki akan wani muhimmin gari dake zama cibiyar masu bijirewa gwamnati a kusa da birnin Homs, inda aƙalla mutane ukku suka sami rauni. Masu fafutuka da kuma mazauna garin sun sanar da cewar cikin dare ne dakarun gwamnati suka kai harin. Birnin Homs ya kasance dandalin yin taho-mu-gama a tsakanin dakarun gwamnati da kuma 'yan adawar dake samun goyon bayan sojojin da suka bijirewa gwamnati, waɗanda ke neman kifar da mulkin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar.

Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta ce tun bayan ɓarkewar boren neman kifar da mulkin shugaba Assad, kimanin mutane 2,700 ne dakarun gwamnatin Siriya suka janyo mutuwar su-ciki kuwa harda ƙananan yara 100. A halin da ake ciki kuma firaministan ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shaidawa tashar telebijin ta CNN cewar ko ba jima-ko ba daɗe al'ummar Siriya za ta kawar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, domin kuwa a cewar sa babu wani mulkin da zai ɗore ta hanyar ƙuntatawa 'yan ƙasa da kuma gallaza musu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu