1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na ci-gaba da yin luguden wuta akan 'yan adawa

April 8, 2012

'Yan adawa a Siriya sun ce sojoji sun kashe mutane fiye da 100 a ci-gaba da farmaki gabanin cikar wa'adin tsagaita wuta a ranar Talata.

This image made from amateur video and released by the Syria media center Thursday, March 29, 2012, purports to show black smoke riding from buildings in Homs, Syria. Syrian President Bashar Assad says he will spare no effort to make the mission of U.N.-Arab League envoy Kofi Annan a success but he demands that armed opponents commit to halting violence. (Foto:Syria Media Center via APTN/AP/dapd) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL. TV OUT
Syrien lehnt Annan-Forderung nach Niederlegung der Waffen ab ACHTUNG SCHLECHTE QUALITÄTHoto: dapd

Akalla mutane fiye da dari daya ne aka bada rahoton sun rasa rayukansu a sassan kasar Siriya a jiya Asabar wadanda suka hada da fararen hula 86 a cigaba da barin wutar da sojin gwamnatin ke yi akan 'yan adawa. Jami'an sa ido na kasa da kasa sun ruwaito cewa dakarun gwamnatin Siriya sun zafafa kai farmaki akan 'yan adawa gabanin wa'adin tsagaita wuta da kuma janyewa wanda zai cika a ranar Talata mai zuwa. Farmakin na cigaba da gudana a daidai lokacin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon a baya-bayan nan ya soki gwamnatin ta Damascus da zafafa kai hare hare, lamarin da yace ya sabawa sharadin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta. Majalisar Dinkin Duniyar ta yi kiyasin cewa mutane fiye da 9,000 ne aka kashe a Siriyan tun bayan barkewar bore shekara guda da ta wuce.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe