1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na fuskanatar barazanar samun karin takunkumi

November 26, 2011

Kungiyar hadin kan Larabawa ta yi barazanar karawa Siriya takunkumi idan har bata nuna amincewarta da sabon wa'adin da ta deba mata ba.

Shugaba Bashar al AssadHoto: picture-alliance/abaca

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar agaji wajen ciyar da akalla mutane milliyan daya da rabi wadanda suka kaurace daga Siriya sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinye suna kuma samun mafaka a kan iyakar kasar da kasashen Turkiya da Lebanon.

Tun farko dai Kungiyar hadin kan larabawa ta sake baiwa Siriya wa'adi na biyu domin ta dakatar da zud jinin fararen hulan kasar da dakarun gwamnati ke yi ba gaira ba dalili, amma kawo yanzu gwamnatin bata mayar da  martani dangane da wannan wa'adi ba, bare ma ta nuna amincewar ta ko akasin haka. Ita dai kungiyar ta sha alwashin kakabawa Siriya takunkumin da zai shafi tattalin arzikin kasar idan har zuwa ranar juma'a da rana bata amince da ziyarar wata tawagar wakilan kungiyoyin kasa da kasa wadda zata sanya ido kan yadda alamura ke gudana. Wa'adin farko da kungiyar ta baiwa Siriya na dakatar da rikicin zai cika a wannan asabar, kuma a na sa ran idan an jima, kungiyar Larabwan zata sake ganawa a birnin Alkahira domin daukan mataki na bai daya akan gwamnatin ta Bashar Al Assad.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita          :  Yahouza Sadissou Madobi