1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na fuskantar barazanar ƙarancin abinci

March 14, 2012

Hukumar abinci kuma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta baiyana fargaban dangane da barazanar da kimanin mutane miliyion daya da rabi sukan iya fuskanta ta ƙarancin cimmaka

Ausschnitt aus: epa03134044 A handout photo made available by the official Syrian Arab News Agency (SANA) shows Syrian President Bashar al-Assad (L) meeting with Alla Alexandrovsaya, chairwoman of the Syrian-Ukrainian Friendship Committee in the Ukrainian Parliament, in Damascus, Syria, 06 March 2012. According to SANA, the meeting took up the recent developments in Syria. EPA/SANA/HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumomin na ayyukan gona da na cimmaka na Majalisar Ɗinkin Duniya na FAO da na PAM waɗanda ke da cibiyoyi a birnin Rome na ƙasar Italiya na ƙaddamar da ayyukan agajin na gaggauwa ga mutane kusan dubu dari a Siriyar sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi wanda kawo yanzu Majallisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane kusan dubu bakwai suka mutu

Hukumar ta ce yankunan da lamarin ya fi ƙamari su ne garuruwan Homs da Hama da Dara'a da kuma Idelb inda wasu duban jama'a suka ficce daga garuruwan,hukumar ta FAO ta ambato wani ofishin ƙididiga na Siriya na mai cewa tsananin hahauwar frashin kayan abinci da ake fuskanta da kuma ƙarancin man feutir ya sa kuɗin sufirin na mota ya ƙaru.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar