1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya na fuskantar matsin lamba

September 6, 2012

Ƙungiyar ƙasashen larabawa ta yi Allah wadai da kisan jama'a da sojojin gwamnatin Bashar Al-Assad ke yi

Egypt's President Mohamed Mursi talks at the Arab League headquarters in Cairo September 5, 2012. Mursi, promising to put Cairo back at the heart of Arab affairs, made an impassioned appeal to Arab states on Wednesday to work for an end to the bloodshed in Syria and said the time had come to change the Syrian government. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Ministocin harkokin waje na ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke ci gaba da gudanar da taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar;sun yi Allah wadai da abin da suka kira kisan gila da gwamnatin Bashar Al Assad ke aiwatar wa akan jama'a,haka kuma ministocin sun buƙaci gwamnatin ta Siriya da ta dakatar da ta'adin.

Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi mai masabkin baƙin wanda ya ce ya zama tilas gwamanatin Bashar Al Assad ta yi marabus ya ƙara da cewar.Ya ce ''ba zamu iya kauda ido ba akan abin da ke faruwa a Siriya, ya kammata mu samu hanyoyin warwware rikicin da gauggawa''.Ƙasashen dai na larabawa sun gargaɗi kwamitin sulhu na MDD da ya gurfana da hukumomin Siriya da na ƙungiyoyin yan gani kashe ni na gwamnati ,a gaban koutun duniya waɗanda ke da hannu a cikin kisan ƙare dangin na Siriya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas