1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma ruwan bam a Idlib na Siriya

Salissou Boukari
September 9, 2018

Jiragen yakin Rasha da ma na gwamnatin Siriya sun soma lugudan wuta a yankin Idlib da ke a Arewa maso yammacin kasar ta Siriya iyaka da Turkiya wanda ya rage a hannun mayaka daga cikin yankunan kasar ta Siriya.

Syrien Idlib Rauch nach Luftangriffen der Regierungskoaliltion
Hoto: Getty Images/AFP/O.H. Kadour

Tun dai daga ranar Asabar ne jiragen yakin suka soma ruwan bama-bamai a yankuna da dama na jihar ta Idleb, yankin da ke da mutanen da yawansu ya kai sama da miliyan uku, daga cikinsu akwai dubban mayaka akasarinsu 'yan jihadi na kungiyar Hayat Tahrir al-Cham tsohuwar kungiyar Al-Qaida a kasar ta Siriya.

A jiya Asabar dai Rasha ta jaddada cewa tana rike da cikokun shedu da ke nunin cewa 'yan tawayen yankin na Idlib na shirin yin wata babbar tsokala, sai dai Rashan ba ta sanar ko wace irin tsokala ce ba, inda ta ce mayakan jihadi na kungiyar Hayat Tahrir al-Cham, da 'yan tawaye na Turkestan da kuma jami'an agaji da ke tare da 'yan tawayen sun yi wani zama a ranar Juma'a inda suka amince kan wani mataki da za su dauka.