Makomar Siriya shekara guda bayan mulkin Assad
December 8, 2025
Ko da yake kawar da Bashar al-Assad ta hanyar farmakin gaggawar da kungiyar Hay'at Tahrir al-Sham ta kaddamar cikin watan Disambar bara, ya dakatar da mafi munin tashin hankali a Siriya, kasar ba ta samu cikakkiyar kwanciyar hankali ba har ya zuwa wannan lokaci.
An dai samu dan saukin matsaloli na tsaro musamman a Damascus babban birnin kasar, amma hare-hare da fafatawa na ci gaba tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin Kurdi da 'yan kabilar Druze da wasu magoya bayan Assad da suka buya, da kuma mayakan IS da ke kokarin sake tasowa.
Rashin doka da ramuwar gayya na ci gaba saboda tsarin sasanta laifukan da aka aikata a baya bai daidaita ba kuma siyasa ta takaita shi. A fannin siyasa kuwa, an fara daukar matakai na gyara: An gudanar da wani zaben wakilai da ba kai tsaye ba, ana kokari na samar da sabon kundin tsarin mulki, sannan an fara tattaunawar kasa.
Amma har yanzu akwai manyan sabani a kan yadda tsarin mulkin a gaba zai kasance, sannan masu suka na zargin shugaban rikon kwarya, Ahmad al-Sharaa, da kokarin tara wa kansa iko abin da ke tayar da hankula cewa kasar na iya komawa tsarin mulkin kama-karya.
A wajen kasashen duniya, sauyin ya fi girma. Siriya ta bude harkokin jakadancinta da hulda da kasashe da dama, har ma ta tura al-Sharaa wanda a da yake cikin jerin sunayen masu tsatsauran ra'ayi da ake takawa kafa ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya kuma ya ziyarci Fadar White House ta Amurka.
Sai dai har yanzu hare-haren Isra'ila a cikin Siriya su ne manyan kalubale, inda suke barazana ga fararen hula da kuma tsari mai rauni na sauyin siyasar kasar.
A bangaren zamantakewa, miliyoyin 'yan Siriya da suka yi gudun hijira sun fara komawa gida, koda yake suna tarar gine-gine burbushin wuta da hanyoyi da makarantun da asibitoci da ke a lalace, da kuma matsanancin karancin ruwa da wutar lantarki da sauran ayyukan gwamnati.
A takaice dai, duk da cewa Siriya ta samu ci gaba a diflomasiyya da dawo da martaba a idon duniya, kasar na fuskantar manyan kalubale a bangaren tsaro da siyasa da zamantakewa da tattalin arziki, kalubalen da za su tantance ko sauyin bayan Assad zai dore ko kuma a'a.