Siriya: Sojojin gwamnati sun kwace Ghouta
April 15, 2018Wannan sanarwa na a matsayin babbar nasara ga gwamnatin ta Shugaba Bashar Al-Assad, kuma na zuwa ne 'yan awoyi bayan da kasashen Amirka, Faransa da Britaniya suka yi lugudan wuta a wasu mahimman wurare uku na gwamnatin ta Siriya, a wani mataki na martani kan zargin da ake yi wa gwamnatin da amfani da makami mai guba kan 'yan tawaye abirnin Douma.
Kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya na SANAA, ya rawaito kalaman wani babban jami'in sojan kasar na cewa sun kakkabe 'yan ta'adda daga yankin gabashin Ghouta gabaki daya. Samamen da sojojin gwamnatin ta Siriya masu samun goyon bayan Rasha suka ayyana a yankin na Ghouta na kusan watanni biyu, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1.700 a cewar kungiyar nan da ke sa ido kan kare hakin bil-Adama a kasar ta Siriya.