1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta amince da wa'adin tsagaita wuta

April 3, 2012

Gwamnatin Assad ta ce ta amince da wa'adin tsagaita wuta a matakin aiwatar da shirin zaman lafiya domin kawo karshen rikicin.

In this image made from video, Syrian President Bashar Assad visits Baba Amr neighborhood in Homs, Syria, Tuesday, March 27, 2012. Assad visited Baba Amr, a former rebel stronghold in the key city of Homs that became a symbol of the uprising after a monthlong siege by government forces killed hundreds of people many of them civilians as troops pushed out rebel fighters. Homs has been one of the cities hardest hit by the government crackdown on the uprising that began last March. (Foto:Syrian State Television via APTN/AP/dapd) SYRIA OUT TV OUT
Hoto: Syrian State Television/AP

Gwamnatin Siriya ta shaidawa wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kasashen larabawa Kofi Annan cewa za ta janye sojoji da manyan tankokin yaki daga matsugunan jama'a a ranar 10 ga wannan watan, abin da ke nufin matakin farko na kawo karshen tarzomar da aka shafe shekara guda ana yi. Sanarwar dai ta zo ne a yayin da sojojin Siriyan suka zafafa farmaki akan 'yan adawa a yankuna da dama tare da lalata gidajensu. A waje guda dai kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da sauran kasashe suna baiyana shakku akan ko shugaban Siriyan Bashar al-Assad zai martaba alkawarin da ya yi.Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniyar Susan Rice ta ce wasu wakilai a kwamitin sulhu sun baiyana damuwa cewa gwamnatin ba za ta yi amfani da yan kwanaki masu zuwa wajen tsananta tarzoma ba.

A na sa bangaren Jakadan Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya bada tabbacin goyon bayan kasarsa ga kudirorin nan shida da Kofi Annan ya gabatar na kawo karshen rikicin. Yace gwamnatin ta jaddada kudirin samun nasarar shirin Kofi Annan ta na kuma yin bakin kokarin na ganin wannan shiri ya yi nasara."

A cikin wannan makon ne dai makon Kofi Annan zai tura tawagar kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu jami'ai zuwa Damascus domin shirya aiwatar da sa ido kan tsagaita wutar.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh