1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta ce ƙasashen yamma ne ke iza wutar rikicin kasar

July 5, 2012

Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya bayyana cewar ya na da cikakken goyon bayan akasarin al'ummar ƙasarsa duk kuwa da cewar wasu na rajin ganin ya kau daga karagar mulki.

Hoto: picture alliance/dpa

Shugaba Assad ya bayyana hakan ne lokacin da yi wata hira da aka buga yau a mujalla Cumhuriyet ta ƙasar Turkiyya inda ya ce ƙasashen yamma ne ke tunzura al'ummar ƙasar wajen gudanar da boren ƙin jinin gwamnatinsa.

Assad ya ce duk da cewar gwamnatinsa ta tafka kusakurai, laifin da ƙasashen ƙetare ke da shi na hannu dumu-dumu a rikin Siriyar ya fi wanda ya tafka inda ya ce in banda goyon bayan da jama'ar Siriya ke ba shi da tuni an kau da shi daga mulki da ƙarfin tuwo.

Baya ga ƙasashen yamma da ya zarga da hannu kan matsalar da ƙasarsa ke ciki, shugaban na Siriya ya zargi Turkiyya da bada taimakon kayan aiki ga masu tada kayar baya, zargin da Turkiyyan ta musanta.

Daura da wannan zargi da Assad ke yi wa Turkiyya da ƙasashen yamma, a gefe guda shafin nan da ya yi fice wajen kwarmata bayanan sirri wato Wikkileaks ya ce nan da ba da jimawa ba zai fidda wasu bayanai daga ciki saƙonnin email miliyan biyu da kusan rabi wanda ke nuna kyakkyawar alaƙa tsakanin Siriya da wasu kamfanonin ƙasashen yamma.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal