Siriya ta mayar da martani ga Erdogan
December 27, 2017![Shugaban kasar Siriya Bashar al- Assad](https://static.dw.com/image/40166200_800.webp)
Talla
Ma'aikatar harkokin kasashen ketaren ta Siriya dai, na mayar da martani ne ga Shugaba Erdogan bisa kalamansa na ayyana shugaban kasar Siriyan Bashar al-Assad a matsayin dan ta'adda. Erdogan ya ce ba ya jin zai iya ci gaba da tattauna batun rikicin Siriyan da Shugaba Bashar al-Assad wanda ya ce ya yi ta'addanci a kan al'ummarsa. Shugaban na Turkiyya ya bayana hakan ne a jawabin da ya yi ga manema labarai a Tunusiya yayin ziyarar aiki da yake a kasar. Kalaman na Erdogan dai su ne mafi zafi da ya yi a kan Assad a dai-dai lokacin da kasashen Turkiyya da Rasha da kuma Iran ke kokarin ganin sun shawo kan rikicin na Siriya da ya lakume rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.