1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta yi fatali da shawarar ƙungiyar larabawa

January 23, 2012

Tsugune ba ta kare ba a kasar Siriya inda shugaba Bashar al Assad ya yi watsi da tayin ƙungiyar ƙasashen Larabawa na miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa don samun masalaha .

Syrian president Bashar Assad adjusts his earpiece during a joint news conference with Spain's Prime Minister Jose Luis Rodriguez Zapatero, unseen at the Moncloa Palace in Madrid Monday July 5, 2010. Assad is on an official visit to Spain. (ddp images/AP Photo/Paul White)
Shugaba Assad ya yi kunnen ƙashiHoto: AP

Hukumomin siriya sun sanya kafa sun shure shawarar da ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta bayar, ta neman shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ya miƙa ragamar tafiyar da mulkin ƙasar ya zuwa hannun mataimakin sa, inda gwamnatin Siriyar ta kwatanta hakan da cewar Shisshigi ne a cikin harkokin cikin gidanta, kamar yadda tashar telebijin ta gwamnatin ƙasar ta sanar. A ranar Lahadin nan ce dai ministocon kula da harkokin wajen ƙungiyar ƙasashen Larabawa suka ƙaddamar da wani sabon yunƙurin neman kawo ƙarshen zubar da jinin da ake yi a cikin ƙasar ta Siriya. Ministocin sun buƙaci shugaba Assad ya miƙawa mataimakin sa harkokin mulki, tare da kafa sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa, wadda za ta tafiyar da mulki - har ya zuwa lokacin gudanar da zaɓukan majalisar dokoki da kuma na shugaban ƙasa. Hakanan kuma ƙungiyar ta tsawaita wa'adin tawagar sanya idon da ta tura zuwa ƙasar, wadda kuma ya zuwa yanzu ba ta cimma wata nasara ba a irin aikin da ta sanya a gaba. Sai dai kuma furucin da hukumomin Saudiyya suka yi game da neman janye wakilan su daga cikin tawagar, ya kawo cikas ga sabon yunƙurin.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Abdullahi Tanko Bala