Siriya: Turkiyya na shirin yi wa Afrin kawanya
March 10, 2018Talla
Tun daga ranar 20 ga watan Janairu ne sojojin na Turkiyya suka ayyana kai hare-hare ta sama a yankin na Afrin da ke arewa maso yammacin kasar Siriya.
A halin yanzu dai sojojin na Turkiyya na kokarin yi wa birnin na Afrin kawanya, bayan da suke rike da kashi 60 cikin 100 na yankin a cewar Rami Abdel Rahmane shugaban kungiyar kare hakin bil-Adama ta OSDH a kasar ta Siriya.
Hare-haren na Turkiyya ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mayaka 370 na Kurdawan na YPG da kuma mayakan da ke mara musu baya sama da 340 a cewar wannan majiya. Sai dai rundunar sojojin kasar ta Turkiyya ta ce sojojinta 42 suka mutu a wannan yaki.