1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Siriya za su mika garuruwansu

Gazali Abdou Tasawa
June 29, 2018

Gwamnatin Siriya da wakillan 'yan tawaye sun soma tattaunawa a wannan Juma'a kan batun mika wasu garuruwan Kudancin kasar da ke a hannun 'yan tawayen ga sojojin gwamnati da nufin kauce wa farmaki.

Angriff des Assad-Regimes auf Daraa, Syrien
Hoto: picture alliance/AP Photo

Rahotanni daga kasar Siriya na cewa gwamnatin Bashar al-Assad da wakillan 'yan tawaye sun soma tattaunawa a wannan Juma'a kan batun mika wa gwamnatin garuruwan Kudancin kasar ta Siriya da ke a hannun 'yan tawayen da nufin kauce wa fuskantar farmakin da sojojin gwamnati suka kaddamar da nufin kwato yankin. 

A ranar 19 ga wannan wata na Yuni ne sojojin gwamnatin Siriya masu samun dafawar sojojin Rasha suka kaddamar da farmaki ta kasa da kuma ta sama a jihar Daraa da ke a hannun 'yan tawaye da kuma ake yi wa kallon tushen bijirewar da aka soma yi wa gwamnatin Al-Assad a shekara ta 2011. 

Da ma dai a kwanaki biyu da suka gabata 'yan tawayen sun mika wa sojojin gwamnatin Siriyar wasu garuruwa uku na jihar ta Deraa a cikin laluma inda su kuma mayakan tawayen aka ba su damar ficewa daga cikin garuruwan inda suka bar tarin manyan makaman da suka mallaka.