Siriya: Za a soma binciken zargin amfani da sinadarin gas
April 17, 2018Kasar Amirka ta baiyana fargaba kan cewa akwai yi yuwar Rasha ta yi kutse a yankin da za a gudanar da wannan binciken abinda ka iya shafar sakamakon duk wani binciken da masanan za su gudanar, zargin da tuni Rasha ta musanta. A karshen makon da ya gabata wasu kasashen yamma da suka hada da Amirka da Britaniya da Faransa suka kaddamar da wasu jerin hare-hare a Siriya a matsayin martani kan zargin da ake wa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da anfani da sinadarin gas mai guba kan fararen hula a yankin na Douma inda mutane kusan dari suka halaka.
A daya bangaren kuwa, ma'aikatar tsaron Siriyan ta yi nasarar kakkabo wasu jiragen yaki masu linzami da aka harba ma ta a yankin Homs a wannan Talata duk da cewa babu kasar da ta dauki alhakin kai harin. Rikicin Siriya na fiye da shekaru shida ya yi sanadiyar rayukan dubban mutane.