Siyasar ƙasar Girka na tangal-tangal
May 16, 2012Shugabannin siyasa a ƙasar Girka sun haƙura da batun kafa gwamnati, bayan jerin tattaunawa da aka yi tsakanin manyan jam'iyun ƙasar, amma aka kasa kafa gwamnati tun bayan zaben da ya gudana kwanaki tara. Hakan dai yana nufin ba makawa za a gudanar da zabe a tsakiyan watan gobe. A yaune ake saran shugaban ƙasar ta Girka zai sanar da ranar yin zaben, kana ya nada gwamnatin wucin gadi. Abinda ya hana akafa gwamnati dai shine banbancin ra'ayi kan bashin EU da asusun IMF na Euro biliyan 130 da aka baiwa ƙasar don ceto tattalin arzikinta. Rikicin siyasan ƙasar ta Girka dai zai iya sa ƙasar ta pice daga cikin ƙasashe masu amfani da kudin Euro. Zaɓen da ya gudana a farkon watan nan ya gaza fidda dan takaran da ya yi nasara tsakanin jam'iyyun da ke goyon bayan shirin tsuke bakin aljihu da masu adawa da tsarin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu