Rikita-rikitar siyasa a Jamhuriyar Nijar
October 15, 2015![Mahamadou Issoufou](https://static.dw.com/image/18282053_800.webp)
Talla
A yayin da zabuka a Jamhuriyar Nijar ke kara gabatowa, ana ci gaba da samun rikicin siyasa, yayin a hannu daya batun kirkiro da sababbin jam'iyyun siyasa barkatai ke ci gaba da shan suka daga 'yan kasar, a daya hannun kuma ana zargin wasu jam'iyyun siyasar kasar har ma jam'iyya mai mulki da rashin mutunta ka'idojin demokaradiyyar.