1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Siyasar Chadi: Deby ya kaddamar da yakin neman zabe

April 15, 2024

Shugaban Chadi Mahamat Deby ya gudanar da gangamin yakin neman zabe a karon farko domin rikidewa zuwa 'dan dimukradiyya, don kawo karshen mulkin soji tare da alkawarin tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arziki.

Shugaban rikon kwaryar Chadi Mahamat Idriss Deby a yayin kada kuri'ar raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar a birnin N'Djamena
Shugaban rikon kwaryar Chadi Mahamat Idriss Deby a yayin kada kuri'ar raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar a birnin N'Djamena Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP/Getty Images

Gwamnatin Mahamat Deby na daga cikin mulkin da sojoji suka kafa da ya ja hankalin kasashen duniya, wanda kuma ya gurgunta tsarin dimukradiyya a kasar da ke yammacin Afrika.

Karin bayani: Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa 

Chadi ce kasa ta farko da ta shirya gudanar da zabe daga cikin kasashen da sojoji ke mulki nahiyar Afrika, duk da kiraye-kirayen kasashen duniya na mika mulki ga farar hula, a zaben da aka shirya gudanarwa a watan Mayun 2024. 

Karin bayani: Kotu ta tantance masu tsayawa takara a kasar Chadi 

A yayin da yake jawabi ga dandazon magoya baya a birnin N'Djamena, Deby ya jaddada cewa za a gudanar da zabe domin dawo da kasar kan tafarkin dimukradiyya tare da tabbatar da cewa zai cika alkawari wajen dora kasar kan gwadabe mai kyau kasancewar sojoji na martaba alkawari musamman batun tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.