1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar jihar Rivers ta Tarayyar Najeriya ta shiga mawuyacin hali

July 19, 2013

Rikicin siyasar jihar Rivers na rikida zuwa wata dama ta siyasa a bangaren gwamnonin da ke son yin kafar ungulu ga burin Shugaba Jonathan na yin tazarce

)
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

A wani abun da ke zaman alamu na irin alkiblar da siyasar Tarrayar Najeriya ke fuskanta, rikicin da ya kai ga tsai da dokacin harkoki a jihar Rivers yanzu haka na shirin komawa dama ta siyasa a bangaren gwamnonin da ke adawa da burin shugaban kasar na zarcewa a bisa gadon mulkin kasar, nan da shekaru biyu masu zuwa.

Rikicin ya kama hanyar yaduwa

Duk da cewar an kai ga zub da jini da ma artabu tsakanin bangarorin da ke neman ganin bayan junansu cikin jihar Rivers, mai arzikin man fetur a Tarrayar Najeriya, sannu a hankali launi da kalar rikicin na kara fita ga dokacin kasar ta Najeriya da ta share tsawon mako guda tana tofin Allah tsine ga rashin dadin da ya faru cikin zauren majalisar dokoki ta jihar. Ko bayan muhawara da ma kokari na dora laifin da ta mamaye dokacin kafafen yada labaran cikin gidan a kusan dokacin makon mai karewa dai, Fatakwal, babban birnin jihar na daukar manyan bakin da ke tururuwar jajen Allah kare ga dan uwansu Rotimi Amaechi. To sai dai kuma ziyarar da aka bude ta da wasu gwamnonin jam'iyyarsa ta PDP biyar da ke Arewa, kafin wasu takwas na kawancen APC da ke adawa su biyo baya dai daga dukan alamu na kara tabbatar da hasashen inda siyasar kasar ta Najeriya ke shirin fuskanta a cikin kankanen lokacin da ke akwai. Duk da dai rai ya baci an kira ba dadi, babu ko da gwamna guda na PDP da ke kudun kasar da ya yarda a hango keyarsa cikin garin da ya kalli jerin zanga-zangogi da ma barazana iri-iri a cikinsa. Ko bayan nan ma babu ko da kalaman an bata a bangaren  jam'iyyar PDP ta kasa da 'ya'yan nata ne ke bai wa hammata iska balle tunani na mataki da nufin sake tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umar jihar.

Hoton Amaechi(hagu) da Sanusi LamidoHoto: DW/U.Haussa

Tasirin ziyarar gwamnoni zuwa Rivers

Tuni dai dama aka fara karanta ziyarar da kokari na sako mai karfi a bangaren gwamanonin da a watan Mayu suka tabbatar da sake zaben Ameachi bisa shugabancin kungiyar gwamnonin kasar mafi tasiri duk da adawa daga fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock.To sai dai kuma a fadar Murtala Hamman Yero Nyako da ke zaman gwamnan jihar Adamawa kuma daya daga cikin gwamnonin da suka share fage da ziyarar da tasirinta ya kai har a kwakwalwar fadar gwamantin kasar babu siyasa a cikin halin da ya kai su jihar ta Rivers.

Barazana ga tsarin ikon shugaban kasa

Garkuwa irin ta karfe ga demokaradiyar Tarrayar Najeriya ko kuma kokari na aika sakon mun kawo karfi dai ana dai ta'allaka dokacin rikicin da sakamakon zaben da ya bata ran mazauna fadar  da kuma a karon farko ke nuna alamu na rashin tabbas ga makomar shugaban kasar a zabukan cikin gidan jam'iyyar na badi.

Matatar mai a Port HarcourtHoto: picture-alliance/dpa

To sai dai kuma martanin da ya kai jihar ya zuwa rikicin da aka jima ba a kalli irinsa ba dai, a cewar Mallam Faruk B. B. Faruk  da ke zaman tsohon shugaban matasan PDP da yanzu haka kuma ke kallon lamuranta a nesa, na zaman babbar barazanar da tsarin kasar na shugaba mai cikakken iko ke yi ga kokari na tabbatar da ginin ginshikan demokaradiya, a tsakanin al'ummar kasar da ke jiran gani a kasa.

Abun jira a gani dai na zaman girman garkuwar da tsarin demokaradiyar kasar ke iya samu da nufin hana masa fadawa tarkon rikicin da ya kai ga ganin bayan yayyensa na baya.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Halima  Balaraba Abbas

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.