1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Siyasar mallakar arzikin mai ta kunno kai a Najeriya

December 29, 2021

Tsohuwar siyasar mallakin man fetir ta sake tashi a Najeriya da ke shirin shiga zabuka kasa da wattani 15. 'Yan siyasar kudanci na cewa hajarsu ce da wasu suka fi su samun amfani.

Erdöllraffinerie in Nigeria
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Sun dai fake da gwagwarmayar mallakin albarkatun kasa, kuma daga dukkan alamu suna shirin dirawa a cikin bakar siyasar da ke ta yin cida cikin kasar a halin yanzu. Kama daga tsoho na shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, da ke kida yana rawa cikin makomar kasar a halin yanzu, ya zuwa Edwin Clark da ke zaman jagora na kabilun yankin Neja Delta, siyasar man fetur na zaman kafa ta siyasa da makomar Tarrayar Najeriya da ke kara kusantar zabe.

Clark din dai ya ambato Obasanjo cikin jerin makiyan al'ummar yankin bayan da abokin takun nasa ya ce man yankin na zaman na mallakin al'umar kasar. A baya dai mallakin man na zaman makami na siyasar kasar, siyasar kuma da ta kalli sauyin fasali da salo iri-iri a lokaci mai nisa. To sai dai kuma sake tado ta kasa da wattani 15, na nuna alamun komawa bisa tsohon yayin amfani da albarkatun kasar wajen biyan bukata ta siyasa.

Edwin Clark din dai alal ga misali ya yi nisa a wajen hankoron mai da mulkin kasar zuwa Kudu maso Kudanci  ko kuma Kudu maso Gabas ta al'umar Ibo. A yayin kuma da Obasanjo ke kokarin daurin gindi ga daya daga cikin 'ya'yan kabilarsa kuma shugaban bankin raya kasashen Afirka Dr Akinwunmi Adesina.

Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Wayon a ci inji karen da ya bar gindin dinya babu shiri, ko kuma kokari na tabbatar da gaskiyar kundin tsarin mulki dai, in har tsohuwar siyasar man fetir ta yi tasiri wajen dora shugabannin kasar can baya, daga dukkan alamu da sauran aiki ga jakadunta a cikin sabon tsarin da kasar ke tafiya kai a yanzu.

An dai bata wa kusan kowane sashe na kasar, sannan kuma shi kansa hajar man fetur din na komawa baya cikin na kan gaba ga dogaro a Tarrayar Najeriyar. An kuma share watanni alal ga misali kamfanin mai na kasar NNPC, na ba da gudummawar da ba ta karya kara ga kudin shigar da ake ta rabawa a kowane wata ba.

Sai dai ita kanta duniyar na dawowa daga rakiyar man fetur a fadar Dr. Ahmed Adamu, masanin makamashi a jami'ar Baze da ke a Abuja. Abin jira a gani dai na zaman makomar Najeriyar, kasar da ta manta da yawan al'uma tare da komawa zuwa ga haja daya tilo da nufin rayuwa maras tabbas.