Siyasar Senegal: An bude rumfunan zaben shugaban kasa
March 24, 2024Kimanin Mutane milyan 7.3 ne sukayi rajistar kada kuri'a a kasar ta Senegal da ke yammacin Afrika. A dokar kasar za a rufe rumfunan zabe da misalin karfe 6 na yamma agogon GMT, inda za a sanar da sakamakon zaben a cikin mako mai zuwa.
Karin bayani: 'Yan takarar shugaban kasa a Senegal sun kaddamar da yakin zabe
Daruruwan masu sa ido ne suka isa Senegal, kasar da ke rike da kambun gudanar da sahihin zabe da kuma bunkasar dimukradiyya a yankin kasashen yammacin Afrika. Rahotannin sun tabbatar da isar masu sa ido daga kungiyoyin fararen hula da kungiyar raya kasashen Afrika ta AU da kungiyar bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS harma da wakilcin kungiyar tarayyar Turai EU.
Karin bayani:Diomaye Faye ya samu goyon bayan Karim Wade a zaben Senegal
Dukkan 'yan takarar da suke shiga zaben sun yi hasashen samun nasara a zagayen farko kama daga dan takarar da ke samun goyon bayan shugaban kasar mai barin gado Macky Sall wato Amadou Ba da 'dan takarar da ke samun goyon bayan Karim Wade da aka haramta masa takara wato Bassirou Diomaye Faye harma da tsohon magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall.