1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Siyasar Senegal da mutuwar shugaban Namibiya a jaridun Jamus

Abdourahamane Hassane MAB
February 9, 2024

Shugaban Senegal Macky Sall ya sha suka a jaridun Jamus bayan da ya dage zaben shugaban kasa i zuwa karshen 2024, yayin da suka nuna alhini game da mutuwar shugaban kasar Namibiya Hage Geingob saboda kishin kasa.

Shugaba Macky Sall ne da kansa ya sanar da dage zaben shugaban kasar Senegal
Shugaba Macky Sall ne da kansa ya sanar da dage zaben shugaban kasar SenegalHoto: RTS/Reuters

Jaridar die Tageszeitung ta wallafa sharhi mai taken "Dimukuradiyyar Senegal na fuskantar barazana", inda ta ce masu adawa da gwamnati sun tabbatar da cewar Shugaban kasa Macky Sallzai ci gaba da zama kan karagar mulki na kusan shekara guda mai yiyuwa, bayan sanarwar da ya bayyana dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga wata Fabrairu saboda kura-kuran da ya ce an gano na takardun haihuwa na bogi na wasu daga cikin 'yan takara.

Karin bayani: Rudanin siyasa a Sengal bayan soke zabe

Tashe-tashen hankula sun biyo bayan sanar da dage zaben SenegalHoto: Seyllou/AFP

Dama dai take-taken da gwamnatin Dakar ke yi ya sa ta rasa yarda ta jama'a, ganin irin yadda tun daga shekarar 2021 jami'an tsaro ke kara yin fito na fito da masu zanga-zangar bayan da gwamnatin ta haramta zanga-zanga da karya dokoki na walwala da 'yanci. Kungiyar Kare kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi kiyasin cewar tun daga watan Janairu ya zuwa yanzu, kusan mutane dubu daya ne ake tsare da su a gidajen yari wadanda har yanzu ba a yi musu sharia'a ba.

Dangantakar Jamus da Senegal ta fara tangal-tangal

Kyakyawan fata da Scholz ya yi na samun iskar gaz daga Sall na daf da wargajewaHoto: Robert Adé/DW

Olof Scholz da ke zama shugaban gwamnatin Jamus na fuskantar kangi da wannan yunkuri na Macky Sall.Wannan shi ne taken da Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi a kan wannan batu, inda ta ce  ana daukar Senegal a matsayin daya daga cikin kasashe mafi kwanciyar hankali a yammacin Afirka wacce ta dade a kan kyakkyawar turba ta dimukuradiyya,

Karin bayani: Jamus na son karfafa alakarta da Snegal 

Amma a yanzu kasar ta Senegal ta kama hanyar zama ta mulkin kama karya. Gwamnatin Jamus ta sa kyakkyawan fata a kanta na samar da makamashin iskar gas daga Senegal, amma yanzu hulda na dab da wargajewa bayan wannan mataki na juyin mulki da Macky Sall ya yi wa dimukuradiyya na dage zaben har zuwa 15 ga watan Disamban 2024.

Wani fasto zai fuskanci shari'a a Kasar Kenya


Taken da Jaridar der Spiegel ta bude sharhinta da cewar ana tuhumar wani shugaban kungiyar asiri da laifuka 191 na kisan kai a Kenya, wanda a cikin watan Afrilun shekara  ta 2023, aka gano wani katafaren kabari mai dauke da gawarwakin mutane 429 a dajin Shakahola na kasar Kenyar. Za a yi wa Fasto Paul Nthenge Mackenzie mai shekaru 41 wanda tsohon matukin taxi ne shari'a kan kisan mabiya darikarsa 191 bayan da aka tuhume shi da laifin ta'addanci da azabtarwa da zalunci kan yara da kuma kisan kai.

Kotun Kenya na tuhumar Paul Mackenzie Ntheng da yin sanadin mace-mace a cocinsaHoto: AA/picture alliance

Karin bayani: An sake kama wani Pastor da kashe mabiyansa a Kenya

An gano jimillar gawarwaki 429 a cikin dajin Shakahola, inda Faston ya rika yin wa'azin ga mabiyansa na yin azumi har a mutu don samun ganawa da Yesu almasihu kafin karshen duniya, wanda ya sanar da cewa tashin duniyar zai faru a watan Agustan shekara ta 2023 da ta riga ta gabata.

Mutuwar shugaban Namibiya na ci gaba da daukar hankali

Marigayi shugaban kasar Namibiya Hage Geingob Hoto: Caitlin Ochs/REUTERS

Namibiya ta yi rashin fitaccen dan kishin kasa wato shugaba Hage Geingob: wannan shi ne taken da Jaridar der Spiegel ta buga sharhinta a kai. Shi Hage Geingob  wanda ake yi wa kallon dan kishin kasa wanda ya yi tsananin adawa da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu a baya,  ya rasu a  ranar 4 ga watan Fabrairu yana da shekaru 82 a duniya a Windhoek babban birnin Namibiya, inda ya yi jinyar cutar daji.

Karin bayani:  Mace 'yar takarar shugaban kasa a Namibiya

Tun a farkon watan Janairun da ya gabata fadar shugaban kasar ta ba da sanarwar cewar binciken likitoci na yau da kullun ya nuna cewar shugaba Hage Geingob na dauke da cutar daji. Kafin ya hau mulki ma a shekara ta  2013, an yi masa tiyata a kwakwalwa a Afirka ta Kudu.