1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi magajin Seehofer a CSU

Zainab Mohammed Abubakar
January 19, 2019

An zabi Markus Soeder a matsayin shugaban jam'iyyar CSU da ke da tushenta a Bavaria, domin maye gurbin tsohon shugabanta kuma ministan harkokin cikin gida na Jamus Horst Seehofer.

CSU Parteitag München
Hoto: Reuters/A. Gebert

Wakilan jam'iyyar ne suka zabi fraiministan na Bavaria a taro na musamma da jam'iyyar ta gudanar a wannan Asabar din. 

Tuni dai Seehofer ya sanar da manufarsa na yin murabus daga shugabancin CSU a watan Nuwamba. Sakamakon koma baya da jam'iyyar ta fuskanta a zabukan kasar da ya gudana a 2017.

Markus Soeder ya nemi hadin kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da ma 'yar uwarata CDU ta Angela Merkel. Ya ce ya zamanto wajibi a bude wani sabon babi na hadin kai tsakanin jam'iyyun don samar da cigaba mai inganci.