Soja da 'yan Biafra sun gwabza a Najeriya
September 11, 2017Talla
Masu fafutikar 'yancin Biafra a Najeriya sun gwabza fada da dakarun sojan kasar a Kudu maso Gabashin Najeriya a ranar Lahadi, inda ake zargin mutane biyar sun halaka, ko da yake jami'an tsaro a Najeriyar sun karyata wannan zargi.
A cewar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra daga Najeriya mambobinta biyar ne suka mutu bayan da suka gwabza da jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da 'yan sanda a kokarinsu na kama Shugaban kungiyar wato Nnamdi Kanu a gidansa da ke garin Umuahia.