Burkina Faso ta nada shugaban kasa
February 10, 2022Paul-Henri Sandaogo Damiba, shi ne wanda ake ganin ya jagoranci juyin mulkin da ya kai ga hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kabore a ranar 24 ga watan Janairun da ta gabata tare da rusa majalisar kasar. Masu rike da madafun ikon kasar, sun shirya samar da wani kudiri da a ciki ne za a shata yadda za a tafiyar da kasar a karkashin gwamnatin riko na wucin gadi.
Duk da cewa wannan ba shi bane karon farko da ake juyin mulki a kasar da ke yammacin Afirka ba, amma ana ganin gazawar Kabore wajen dakile hare-haren kungiyoyi masu tayar da kayar baya, da aiyukansu ya salwantar da dubban rayuka da hana zaman lafiya ne, suka fusata sojojin kwace mulki daga hannunsa. Tuni Kungiyar Tarayyar Afirka ta kori Burkina Faso daga cikin kungiyar a sakamakon wannan juyin mulkin.