1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan gwamnatin Siriya na kai farmaki

Usman ShehuMarch 24, 2012

Dakarun gwamnatin Siriya sun ƙarfafa farmakin da suke kaiwa yakunan da 'yan tawaye suka fi ƙarfi

In this picture taken on Tuesday March 20, 2012, a destroyed Syrian army tank which was attacked during clashes between the Syrian government forces and the Syrian rebels, in Rastan area in Homs province, central Syria. Syrian troops shelled and raided opposition areas and clashed with rebel fighters around the country Thursday despite U.N. efforts to stop the bloodshed so aid could reach suffering civilians. Activists cited the fresh violence in dismissing a U.N. Security Council statement calling for a cease-fire to allow for dialogue between all sides on a political solution. The government of President Bashar Assad also played down the statement, saying Damascus is under no threats or ultimatums. (Foto:AP/dapd)
Syrien Bürgerkrieg Krieg Panzer Rastan 20.03.2012Hoto: AP

Dakarun gwamnatin Siriya sun yini a yau suna kai farmaki kan inda yan tawaye suka fi ƙarfi. Shaidu sukace, sunga tankokin yaƙi soji suna tacilla rokoki a yammacin ƙasar.

Sabin alkalluman MDD, sun ce akalla mutane dubu 100 ne na kasar Siriya suka shiga halin gudun hijira a kasashe makwabta, musamman a ƙasar Turkiyya da Jordan sakamakon bata kashin da ake tsakanin dakarun gwamnatin Bashar Al-Assad da 'yan taway,e, wanda ya zuwa yanzu yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 10 daga bangarorin biyu. A nasu gefe kasashen duniya na cigaba da matsa kaimi ga shugaba Bashar-Al Assad, wanda ke da goyan bayan Rasha da China. A taron da suka shirya jiya birnin Brussels, ministocin harakokin wajen na kashen kungiyar tarayya Turai, sun kara tsuke takunkumi ga kasar Siriya.Ya zuwa yanzu mutane 126 ne, da suka hada da Bashar Al-Assad na na hannun damarsa aka haramtawa shiga kasashen Turai, sannan kuma aka saka takunkumi ga kudaden da suka mallaka a cikin bankunan kasahen EU. A safiyar yau tsofan sakarae Janar na MDD Kofi Annan da Majalisar ta dorawa yaunin shiga tsakanin rikicin Siriya, ya sauka a birnin Mosko na kasar Rasha, domin ganawa da hukumomin kasar game da batun.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tank Bala