1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan Nijar sun yi artabu da Lakurawa a iyaka da Najeriya

Issoufou Mamane Abdoulaye Mamane
November 26, 2024

Jami'an tsaron jamhuriyar Nijar sun yi wa mayakan kungiyar 'yan ta'addan nan da ake kira Lakurawa luguden wuta a yankin Muntseka na garin Konni mai iyaka da Najeriya

Sojojin Nijar masu yaki da 'yan ta'adda
Sojojin Nijar masu yaki da 'yan ta'addaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A cikin wata sanarwar da rundunar tsaron Nijar ta fitar a kafofin yada labarai mallakar gwamnati, sojojin Nijar din sun sanar da cewa jirage maras matuka sun hango ayarin baburan 'yan ta'adda da dama, wanda kuma aka bibiya tun daga kasar Mali har zuwa kan iyakar Nijar da Najeriya.

Karin bayani : Shirin sake rubuta tarihin Jamhuriyar Nijar

Rundunar sojojin Nijar din ta yi wa 'yan ta'addan kwantan-bauna a yankin Muntseka na gundumar Konni ta jihar Tahoua mai iyaka da Najeriya, inda ta tabbatar da kashe 'yan ta'addan Lakurawa, kana wani mazaunin yankin Umar Sayadi, ya tabbatar da harin inda ya ce. "Sun fito daga iyaka da kasar Mali kuma ana bibiyar tafiye-tafiyen da suke har suka shigo a yankin Konni na jamhuriyar Nijar, daga nan aka kai musu hari tare da kashe kimanin 10 daga ciki, an samu makamai da nakiyoyi da bindigogi tare da lalata ababen hawan da suke amfani da su."

Tuni mazauna yankin Muntseka mai iyaka da Najeriya yankin da aka yi artabu da Lakurawan suka nuna jin dadi kan matakin kai wa 'yan ta'addan hari, a daidai lokacin da rundunar tsaron kasar ke fuskantar kalubale. Abbas wani mazaunin yakin ya ce "Mun ji dadi da kisan 'yan ta'adda da aka yi fiye da yadda kuke zato, muna rokon Allah ya kara tona asirin bata gari." 

Sojan Nijar a fagen dagaHoto: ISSOUF SANOGO/AFP

Karin bayani : Kungiyar AES ta soke kudin Roaming na kiran waya

Tun bayan juyin milkin da sojoji suka yi a Nijar, dakarun tsaron Nijar ke samun masu kushe nasarorin da kasar ke yi a fannin yaki da 'yan ta'adda. Masana al'amuran kasa da kasa irin su Issia Mahaman na ganin ya dace kasashen biyu su hada karfi da karfe domin dakile wannan matsalar. "Yanzu tsakanin da Najeriya dole sai an hada hannu waje daya don yakar ayyukan ta'addanci, domin duk yakin da Nijar ke yi idan Najeriya ba za ta kama ba, cin nasara a yakin ba za ta yiwuwa ba."

Ko a wannan Talata, 'yan ta'addan Lakurawan sun yi wani kutse a kasar Nijar ta yankin birnin Konni, yunkurin da dakarun sojan Nijar suka dakile.