Soji hudu sun rasa ransu a Mali
April 2, 2021
Talla
Wani harin da ake zargin masu ikirarin jihadi da kaddamar da shi ya halaka dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali. Rundunar MINUSMA ita ce ta tabbatar da kisan dakarun na Majalisar Dinkin Duniya hudu yayin da wasu sojoji da dama suka jikkata. Harin dai ya afku ne a wani wuri mai nisan kilomitoci 200 da kan iyakar kasar ta Mali da Aljeriya.
Dakarun sun ce mayakan dauke da muggan makamai sun yi yunkurin kutsa kai a sansanin sojin da ke Aguelhok na arewacin Mali inda suka hana su shiga tare kuma da halaka 'yan ta'addan guda biyar.