1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
October 31, 2022

Rundunar sojan Najeriya ta yi nasarar dakile harin ta'addanci a barikin Wawa da ke jihar Neja, tare da nasarar kashe mahara akalla guda takwas.

Nigeria | Sicherheitskräfte in Jangebe
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Wasu majiyoyin tsaron da ba su so a ambaci sunansu ba sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar, an kai harin ne da niyar kubutar da daruruwan 'yan ta'adda da sojan Najeriya ke tsare da su a barikin.

Rahotanni na cewa da akwai 'yan ta'adda fiye da dubu daya da 500 da ke rike a hannun jami'an tsaron Najeriya a barikin na Wawa ta jihar Neja. Ko a cikin watan Yulin wannan shekarar ta 2022 mai dai, kungiyar ISWAP ta kai wani mummunan hari tare da kubutar da mambobinta da dama da ke tsare a gidan yarin Kuje mai cikakken tsaro da ke Abuja babban birnin kasar.

Wannan lamarin na zuwa ne a yayin da a wannan Litinin din shugaban kasar Muhammadu Buhari ke jagorantar taron gaggawa na majalisar zartarwar gwamnati kan batun tsaro da ke kara ta'azzara a baya-bayan nan a Najeriya.