1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojin Amurka sun kammala fice wa daga Jamhuriyar Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 16, 2024

Bayan hambarar da shugaba Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin bara ne sojojin suka nemi Amurkawan su fice daga kasar

Hoto: AFP

Amurka ta sanar da kammala kwashe dakarun sojinta da ke Jamhuriyar Nijar a Litinin din nan, bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka bukaci ficewar ta su.

Karin bayani:Nijar ta kori Amurka saboda barazanar takunkumi a kan Iran

Sojojin Amurka sama da dubu daya ne suka yada sansani a birnin Agadez, inda suka ajiye jirage marasa matuka, a wani bangare na yaki da ayyukan ta'addanci a kasashen Sahel da ma yankin yammacin Afirka.

Karin bayani:Sojojin Rasha sun canji na Amurka a Nijar

Bayan hambarar da shugaba Mohamed Bazoum da tsinin bindiga a ranar 26 ga watan Yulin bara ne sojojin suka nemi Amurkawan su fice daga kasar, nan take Amurka ta amince da kwashe komatsanta ta yi gaba, ba tare da nuna wata tirjiya ba.