Sojin Birtaniya za su ci gaba da zama Afganistan
October 27, 2015Kasar Birtaniya ta bada sanarwar cewa rukunin sojojinta da ya yi saura a Afganistan zai ci gaba da kasancewa a wannan kasa a shekara ta 2016. Ministan tsaron kasar ta Birtaniya Micheal Fallon ne ya sanar da hakan a wannan Talata inda ya ce sojojin Birtaniyar su 450 da suka yi saura za su cigaba da bayar da horo da kuma shawarwari ga sojin kasar ta Afganistan.
A shekarar ta 2014 ne dai bayan kwashe sheku 13 na yaki da Kungiyar Taliban inda sojojinta 456 suka halaka, Birtaniyar ta kwaso mafi yawa daga cikin sojojinta 9500 da ta jibge a kasar ta Afganistan a farkon yakin zuwa gida.
Wannan mataki na hukumomin kasar Birtaniyar ya zo ne kwanaki kalilan bayan da Shugaban Amirka Barack Obama ya bada sanarwar ci gaba da zaman sojojin kasar tasa a kasar ta Afganistan a shekara ta 2016 domin ci gaba da kalubalantar mayakan Kungiyar ta Taliban da ke ci gaba da mallakar ikon wasu yankunan kasar.