Sojin Kanada 6 sun rsa rayukan su a Afghanistan
April 9, 2007Wasu sojin kasar Kanada 6 a Afghanistan, sun rasa rayukan su wasu kuma biyu sun jikkata.
Hakan a cewar rahotanni nada nasaba ne da fashewar wani bom ne daya tashi da motar da suke ciki ne a kudancin kasar.
Kafafen yada labarai dai sun rawaito wani jami´i daga ma´aikatar tsaron kasar a birnin Ottawa na cewa, wannan al´amari ya faru ne a yammacin kasar ta Afghanistan daf da kusa da birnin Kandahar.
Wannan dai hari a cewar bayanai ya kasance mafi muni ga dakarun sojin kiyaye zaman lafiya a kasar, a cikin yan watannin nan.
Dakarun sojin dai na Kanada na gudanar da aikin kiyaye zaman lafiyar ne a Afghanistan karkashin kungiyyar laimar tsaro ta Nato.
Arangama dai a tsakanin dakarun tsaron na Nato da kuma tsagerun kungiyyar Taliban, a yan kwanakin nan abu ne dake ci gaba da yin tsamari a kasar ta Afghanistan.