Sojin Libiya sun kwace birnin Sirte da IS
December 5, 2016Talla
Tuni ma dai gwamnatin hadin kan kasar ta bayyana gamsuwarta da maido da wannan birnin wanda ya ke mahaifar tsohon shugaban kasar marigayi Kanal Gaddafi a karkashin ikonta. Kakakin rundunar sojin gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya a birnin na Sirte Reda Issa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa a yanzu sun karya lagon kungiyar ta IS daga cibiyar tata ta birnin Sirte inda da dama daga cikin mayakanta su ka yi saranda tare da mika wuya.
Sai dai sojojin gwamnati kimanin 700 ake kyautata zaton sun kwanta dama a yayin da wasu dubu uku suka ji rauni a cikin fadan wanda ya bada damar kwato birnin da ya fada a hannun Kungiyar ta IS a watan Yunin shekarar 2015.