Sojin MDD sun fara janyewa daga Kwango
February 28, 2024Talla
A yayin bikin da aka gudanar a hukumance a sansanin Kamanyola da ke kusa da iyakar Rwanda da Burundi, an maye gurbin tutar Majalisar Dinkin Duniya da Pakistan wadanda sojojinsu na kiyaye zaman lafiya ke kula da sansanin.
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta bukaci janye dakarun kiyaye zaman lafiyar duk da damuwar da Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna kan yawaitar tashe tashen hankula a gabashin kasar Kwangon