1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Sojin Mexico sun kashe gawurtacen mai safarar muggan kwayoyi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 23, 2026

Mexico ta samu nasarar halaka jagoran 'yan kwayar mai suna El Mencho bisa tallafin bayanan sirri da ta samu daga Amurka.

Sintirin jami'an tsaron Mexico a birnin Mexico City ranar 22.02.2026 batan kashe El Mencho
Sintirin jami'an tsaron Mexico a birnin Mexico City ranar 22.02.2026 batan kashe El MenchoHoto: Daniel Cardenas/Anadolu/picture alliance

Rundunar sojin Mexico ta sanar da kashe gawurtaccen mai safarar muggan kwayoyi da ya yi kaurin suna, wato Nemesio Oseguera da aka fi sani da El Mencho, bayan wani gagrumin samame da sojojin suka kai maboyarsa a ranar Lahadi, wanda ya tayar da hargitsi a fadin kasar.

El Mencho, wanda shi ne jagoran gungun masu dillancin kwayoyi na Jalisco New Generation Cartel, ya samu munanan raunuka sanadiyyar artabu da sojojin a garin Tapalpa na jihar Jalisco, inda ya cika a kan hanyar kai shi Mexico City babban birnin kasar.

Karin bayani - Dan bindiga ya bude wuta a filin wasan kwallon kafa a Mexico

Bayan kama shi ne 'yan bindiga suka tare manya tituna sama da 20 na  jihar Jalisco, suna kona motocin jama'a, tarzomar da ta fantsama zuwa jihohi takwas na kasar, dalilin da ya sa shugaba Claudia Sheinbaum kira ga al'ummar kasa su rungumi zaman lafiya.

Mexico ta samu nasarar halaka jagoran 'yan kwayar bisa tallafin bayanan sirri daga Amurka, in ji mai magana da yawun fadar mulkin Amurka White House Karoline Leavitt.

Karin bayani - A karon farko mace na shirin lashe zaben shugaban kasa a Mexico

Kuma shi ne na uku da ya shiga hannun jami'an tsaro, bayan Joaquin Guzman da aka fi sani da El Chapo da kuma Ismael Zambadara, wadanda ke zaman gidan yari a Amurka yanzu haka.